Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa babu wani lokaci da aka tsayar don ƙaddamar da rahoton Steve Oronsaye.
Da yake magana bayan wata ziyarar aiki da ya kai hedkwatar hukumar da ke sa ido kan kudaɗen shiga da ake samu wajen haƙƙo ma’adinai (NEITI) a Abuja, Gbajabiamila ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na aiki tuƙuru kan rahoton tare da musanta cewar an ajiye rahoton kuma ba za ayi amfani da shi ba
Ya kuma jaddada buƙatar yin taka-tsantsan, inda ya bayyana cewa yayin da aka kafa kwamitin da zai duba rahoton, za a fara aiwatar da shi nan ba da daɗewa ba.
Rahoton Oronsaye, wanda aka gabatar a shekarar 2012, ya ba da shawarar ragewa tare da haɗa ma’aikatu, kwamitoci, da hukumomi 541 na Najeriya ta hanyar rage su zuwa 161, da haɗe 52, da kuma soke 38 don rage kashe kuɗin gwamnati da kuma tabbatar da inganta ayyuka.
Don haka ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da aiwatar da rahoton gadan-gadan a cikin watan Fabrairu a wani ɓangare na matakan rage tsadar kayayyaki, aiwatarwar na samun tafiyar hawainiya.
Amma duk da cewa an kafa kwamitin mutum takwas domin aiwatar da shirin cikin mako 12, sai dai an yi wata shida ke nan kuma babu wani muhimmin mataki da aka ɗauka.
Maimakon haka, gwamnati ta kafa ma’aikatar kula da kiwon dabbobi daga ma’aikatar noma, wanda hakan ya jawo ra’ayoyi mabambanta.
Rahoton ya samo asali ne daga kwamitin da shugaban ƙasa na wancan lokacin Goodluck Jonathan ya kafa a shekarar 2011 domin magance matsalolin da hukumomin gwamnati ke fuskanta inda Oronsaye ne shugaba kwamiti ɗin.