Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce sabanin rahotannin da ake yadawa cewa, an tsare shi a filin tashi da saukar jiragen sama na Burtaniya, an dakatar da shi ne don duba shige da fice na yau da kullum.
Jami’an shige da fice na Burtaniya sun tsare tsohon gwamnan jihar Anambra na sa’o’i a filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan.
Sai dai a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a daren ranar Litinin, Obi ya dage cewa ba a taba kama shi ba, yana mai jaddada cewa binciken shige da ficen da aka saba yi bai wuce mintuna 20 ba.
Ya ce an duba shi ne kawai saboda ga dukkan alamu wani ne ya kwafi sunan sa.
Obi ya ce, “An dakatar da ni ne don duba shige da fice na yau da kullun a Burtaniya, saboda ga dukkan alamu wani ne ya kwafi kaina. Ba a taba kama ni ba. An girmama ni kuma na bi ta hanyar VIP. Komai bai wuce mintuna 20 ba.”