fidelitybank

Ba a mika mana shedar kofin umarnin kotu na korar gwamna da mataimakin sa – INEC

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce har yanzu ba a mika mata takardar shedar kofi na ainihin da babban kotun tarayya da ta kori Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da mataimakinsa, Cif Kelechi Igwe.

Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Abuja ranar Talata.

Okoye ya ce, hukumar za ta gana kuma za ta yanke hukunci idan ta samu kwafin gaskiya na hukuncin kotun.

“Ba a ba hukumar kwafin hukuncin da aka ce ba. Hukumar za ta gana kuma za ta yanke hukunci idan aka ba ta kofin hukuncin na ainihi,” in ji Okoye.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Ekwo, a ranar Talata, ta umurci Gwamna Umahi da ya bar ofishin, bayan ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Mai shari’a Ekwo, a hukuncin, ya kuma umarci Dr Eric Igwe da ya daina bayyana kansa a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

nnn hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp