fidelitybank

Ba a kama dan Najeriya da kwaya ba a aikin Hajjin bara – NDLEA

Date:

Mataimakin kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, Musa Sani Bakura, ya bayyana cewa, Najeriya ba ta samu matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ba a lokacin aikin hajjin bara.

Ya ce hukumar ba ta samu korafe korafe daga hukumomin Saudiyya na ‘yan Najeriya da ke fitar da kwayoyi ko kuma an kama su da kwayoyi ba.

Shugaban hukumar ta NDLEA ya bayyana cewa a aikin Hajjin bana, sun dauki kwakkwaran matakai na tabbatar da cewa babu wanda ke safarar kwayoyi zuwa kasa mai tsarki, ciki har da masu fitar da goro a cikin manya-manyan, wanda kuma aka haramta.

Karanta Wannan: Mahajjata miliyan 2 za su yi aikin bana a Saudiyya

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano ta fara gangamin wayar da kan Alhazai na shekarar 2023 kamar yadda aka ce hukumar ta samu sama da kashi 70 cikin 100 na ajiya na aikin Hajji.

Da yake jawabi yayin wani taron wayar da kan jama’a da hukumar ta shirya, Sakataren zartarwa, Muhammad Abba Dambatta, ya ce gwamnatin jihar Kano ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da ayyukan Hajji da ke tafe ba tare da tangarda ba.

Dambatta ya yi nuni da cewa Kano ta samu guraben aikin Hajji 5,902 daga Hukumar Alhazai ta kasa, NAHCON, a shekarar 2023, kuma daga cikin su kusan 4000 sun ajiye kudadensu, wanda hakan ya nuna cewa sun jajirce wajen gudanar da shirye-shiryen.

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Amin Ado Bayero, ya ce kwakkwaran matsayar da hukumar jin dadin alhazai ta Kano da gwamnati suka dauka ya taimaka matuka gaya wajen ganin an samu matsala a bara.

Ya bukaci maniyyatan 2023 da su kara zage damtse wajen addu’o’i domin Najeriya ta fita lafiya daga matsalolin da take fuskanta.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp