Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, ta ayyana Lahadi a matsayin ranar 1 ga watan Zulƙi’ida na shekarar hijira ta 1444, wadda ta yi daidai da 21 ga watan Mayun 2023.
Matakin ya biyo bayan rashin ganin jaririn watan a ranar Juma’a da dare, abin da ya sa yau Asabar ta zama 30 ga watan Shawwal.
Hakan na nufin an zo ƙarshen watan da Musulamai suka yi bikin Ƙaramar Sallah a faɗin duniya, wadda ake yi bayan kammala azumin watan Ramadan.
Ranar 10 ga watan Zulhijja – bayan Zulƙi’ida – al’ummar Musulamai daga sassan duniya za su taru a birnin Makkah na Saudiyya don gudanar da ibadar aikin Hajji ta shekarar 1444 ko kuma 2023.