Kocin Crystal Palace Patrick Vieira ya ce, ba a bai wa bakaken fata masu horaswa dama ne a Premier.
Patrick Vieira shi ne koci daya tilo da yake koyar da wata kungiya a gasar Premier, ya ce akwai bukatar bayar da dama ga bakaken yan wasa domin gwada sa’arsu a aikin koyarwa.
Wani sabon rahoto ya nuna cewa kashi 43 na yan wasan Premier da 34 na masu buga sauran wasannin Igila bakake ne, sai dai kashi 4.4 ne kacal ke cikin harkokin horaswa.
“Dole mu bai wa sauran mutane dama,” kamar yadda Viera ya shaida wa BBC.
“Mu ma muna da kyau sosai mun san memuke kamar sauran mutane. kuma da bukatar a dauke mu daidai da kowa.”


