Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya ce, ya kadu sosai bayan rahotannin da ya samu na kadarin jirgin na Shugaba Ebrahim Raisi.
Tun da farko Shugaba Aliyev ya kasance tare da shugaban na Iran waen bikin bude madatsun ruwa biyu a kusa da iayakar Iran din da Azerbaijan.
Shugaban ya ce, “A yau bayan mun yi sallama da Shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta Iran, Ebrahim Raisi, hankalinmu ya tashi bayan labarin da muka samu na hadarin jirgin sama mai saukar ungule da ke dauke da tawagar ta Iran,” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na X.
“Muna addu’a ga Allah ga Shugaba Ebrahim Raisi da tawagar da ke masa rakiya”.
Shugaban ya kara da cewa kasarsa a shirye take ta nayar da dukkanin taimakon da ake bukata.