Hamshakin attajirin nan na Najeriya kuma hamshakin dan kasuwa, Femi Otedola a halin yanzu yana ci gaba da yaduwa a dandalin sada zumunta na Twitter, bayan ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar All Progressives Congress (APC) Bola Tinubu.
Otedola ya ziyarci Tinubu a birnin Paris na kasar Faransa, inda ya raba hoton su a shafukan sada zumunta.
Yayin da yake bayyana jin dadinsa kan ziyarar, dan kasuwar, ya bayyana Tinubu a matsayin babban abokinsa tare da yi masa adduâar Allah ya biya shi, burinsa na zama shugaban kasar Najeriya.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: âA koyaushe ina farin cikin ziyartar Babban Abokina Asiwaju Ahmed Bola Tinubu @officialABAT Allah ya biya masa burinsa na zama shugaban wannan kasa mai girmaâĤF.Oteâ
Hakan dai ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda âyan Najeriya da dama suka nuna rashin jin dadinsu a kan hakan, inda suka bayyana cewa Otedola na goyon bayan Tinubu ne domin cin gajiyar kasuwancinsa.