Shugaban ɗaya daga cikin manyan bankunan Qatar, Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani, ya tabbatar da da cewa gidauniyarsa na shirin sayen ƙungyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United.
BBC ta kuma gano cewa mamallakin kamfanin Ineos, Sir Jim Ratcliffe, shi ma ya taya ƙungiyar a ranar Juma’a
Biloniya Ratcliffe,ya taɓa bayyana sha’awarsa ta sayen ƙungiyar.
Iyalan Glazer, waɗanda suka sayi ƙungiyar a shekarar 2005, na duba yiyuwar sayar da ita, a yayin da suke ƙoƙarin zuba jari a wasu fannonin.
Sheikh Jassim ɗan asalin Qatar ya ce: “Burina shi ne dawo da martabar ƙungiyar kamar yadda take a baya’
”Za mu gyara ƙungiyar ta hanyar zuba jari wajen sayen ‘yan wasa, da gyara wuraren bayar da horo, da filin wasa tare da bunƙasa abubuwan jin daɗi na ƙungiyar”.
“Manufar sayen ƙungiyar ita ce sake dawo da ƙarfinta a fagen wasanni tare da mayar da ita babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa a faɗin duniya”.