Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana inda ya ke.
Atiku ya bayyana cewa zai kasance a birnin Landan daga ranar Litinin zuwa Laraba domin ganawa masu muhimmanci da gwamnatin Birtaniya.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake watsi da rahotannin da ke cewa ba shi da lafiya kuma an garzaya da shi kasar waje domin neman lafiya.
Da yake magana ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, Atiku ya ce yana da hazaka kuma mai tausayi.
Ibe ya rubuta cewa: âDon kaucewa shakku, dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya (1999-2007) zai isa birnin Landan a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu domin ganawa a ranakun Talata da Laraba bisa gayyatar gwamnatin Birtaniya. .â