Tsohon Sanatan Abia, Adolphus Wabara, ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha alwashin sakin Nnamdi Kanu idan ya hau kujerar shugaban kasa.
An kama Nnamdi Kanu ne a kasar Kenya da ke gabashin Afirka kuma aka cusa shi cikin Najeriya sama da shekara guda da ta gabata kuma shugaban haramtacciyar kasar Biafra (IPOB) ke tsare tun lokacin.
Wabara, wanda shine shugaban kwamitin amintattu na jamâiyyar PDP, a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jamâiyyar a Umuahia, babban birnin jihar Abia a ranar Asabar, ya ce Atiku ya yi alkawarin sakin shugaban na IPOB.
Ya ce za a saki Kanu a cikin kwanaki dari na farko na gwamnatin Atiku.
âAtiku ya yi alkawarin sakin danmu daga gidan yari a cikin kwanaki dari na gwamnatinsa. Ba ya tsoron kowa. Zai yi abin da ya alkawarta,â in ji Wabara.
Wabara, wanda tsohon shugaban majalisar dattawa ne daga karamar hukumar Ukwa ta yamma a jihar Abia, ya bukaci alâummar jihar Abia da su zabi dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP a ranar 25 ga watan Fabrairu.