Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yana mai cewa zai karbi ragamar shugabancin jam’iyyar APC a shekarar 2023.
Gwamnan wanda ya zanta da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya isa filin jirgin saman Yola daga hutun makwanni biyu da ya yi, ya ce, babu masu neman shugabancin kasar da ke da halayen shugabanci da za su kayar da Atiku.
Fintiri ya ce, “Siyasa ta cikin gida ce, don haka dole ne ku fara daga wannan matakin don kare muradun jama’ar ku.
Gwamnan ya kara da cewa, halin da kasar ke ciki na bukatar gogaggen mutum wanda zai iya dawo da Najeriya kan turba, ya kara da cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2019 (Atiku) yana da karfin sake hada kan ‘yan Najeriya.