Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na aza harsashin magudin zaben 2023 ta hanyar tattara sakamako da hannu.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye a wata hira da jaridar Punch a ranar Asabar ya ce, za a gudanar da tattara sakamakon zaben shekarar 2023 da hannu duk da amincewar da aka yi ta hanyar amfani da na’urar tantance sakamakon zabe.
An ruwaito Okoye yana cewa “Sashe na 60(5) na dokar ya zama wajibi shugaban hukumar ya mika sakamakon zaben da suka hada da jimillar adadin wadanda aka tantance da kuma sakamakon kuri’un ta hanyar da hukumar ta tsara. Bayan haka, shugaban hukumar bayan nadawa da bayyana sakamakon zai bayar da makamantan kayayyakin zabe a karkashin tsaro tare da rakiyar ’yan takara ko wakilansu, inda za a samu wanda hukumar ta tsara.
“Ma’anar wannan ita ce har yanzu tsarin tattara sakamakon na kan hannu ne, amma jami’in tattara sakamakon dole ne ya tattara sakamakon bincikensa tare da tabbatar da cewa adadin wadanda aka amince da su da aka bayyana kan sakamakon da aka tattara daidai ne kuma sun yi daidai da adadin wadanda aka amince da su. Ya kara da cewa an rubuta kuma ana yada shi kai tsaye daga rumfunan zabe.
Atiku, wanda ya ke mayar da martani ta bakin mai magana da yawunsa, Daniel Bwala Sunday, ya yi zargin cewa, da irin wannan furucin “INEC na aza harsashin magudin zaben 2023”.


