Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ofishin shugaban kasa yana bukatar mutumin da ba shi da inda-inda.
A cikin wata sanarwa da ya saka wa hannu, Atiku ya bayyana cew,a matakin farko da duk wani ɗan takarar babban muƙami ya kamata ya ɗauka a mulkin dimokraɗiyya shi ne ya zaɓi mataimaki.
Ana kallon wadannan kalamai na Atiku a matsayin shaguɓe ga takwarorinsa na wasu jam’iyyu, musamman jam’iyyar APC da NNPP da LP, da har yanzu ba su zabi mataimakansu na dindindin ba.
“Ofishi musamman irin na shugaban ƙasa na buƙatar mutumin da ba ya inda-inda wurin ɗaukar mataki,” in ji Atiku.