fidelitybank

Atiku ya soki Tinubu a kan hana ƴan ƙasa da shekaru 18 zana jarabawar kammala sakandare

Date:

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo koma baya ga harkar ilimi a Najeriya

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin “zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi” inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa’idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi.

Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa.

Ya yi ala-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa da kuma ɓata tsarin gwamnati.

Atiku ya ce, ‘Wannan sabon tsari na gwamnati ba zai yi tanadi ga dalibai masu hazaƙa ba, wanda hakan ke nuna rashin mutunta hazaƙar ilimi.”

“Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen zaƙulo ɗalibai masu hazaƙa tare da tallafa musu, ba tare da la’akari da shekarunsu ba” Atiku ya kara da cewa.

Atiku ya buƙaci da a bar wa gwamnatocin jahohi kula da harkokin ilimi, wanda a tunaninsa zai fi dacewa da yadda ake yi a ƙasashen duniya.

tribune newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp