Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya shigar da wata sabuwar kara a gaban kotun kasar Amurka da ke yankin Arewacin jihar Illinois a kasar Amurka, kan shugaban kasa Bola Tinubu bayan ya janye karar da ake yi a baya.
Ku tuna cewa kotun karamar hukumar da ke jihar Illinois ta yi watsi da karar da Atiku ya shigar, yana neman a saki bayanan karatun Tinubu a Jamiâar Jihar Chicago.
Atiku ya kai karar Jamiâar Jihar Chicago (wanda ake kara) gaban kotu, inda ya nemi a ba shi umarnin tilasta wanda ake kara ya saki bayanan karatun Tinubu a hannunta.
Sai dai a cewar Phrank Shaibu, mataimaki na musamman kan hulda da jamaâa ga Atiku, korar ta biyo bayan janye karar da shugaban makarantar ya yi.
Arisenews ta ruwaito Shaibu ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake mayar da martani game da korar karar da kotun daâar yankin Cook ta yi.
Shaibu ya ce, âWaziri Atiku Abubakar ya janye karar ne kawai a gaban wata kotun daâar da ke gundumar Cook da ke gundumar Illinois ta Amurka, saboda yana gudanar da irin wannan lamari a wata babbar kotu kuma yana so ya kaucewa cin zarafin kotu. Don haka, wannan mafari ne kawai.â
Ya kara da cewa abin dariya ne yadda Tinubu da magoya bayansa suka yi murna da wannan ci gaba kamar dai hukuncin kotun koli ne.