Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu kuri’u 427,611 a jihar Adamawa inda ya doke sauran ‘yan takara a can.
Sakamakon kananan hukumomi 21 da aka sanar a karshen taron a Yola a ranar Litinin da yamma, ya nuna cewa dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Ahmed Tinubu, ya samu kuriâu 182,881.
Mista Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, LP, ya samu kuri’u 105,648.
Haka kuma a sakamakon karshe da jamiâin tattara bayanan na jihar, Farfesa Mohammed Laminu ya sanar, jimillar kuriâu 3,398 ya samu Dumebi Kachiku na jamâiyyar African Democratic Congress (ADC), yayin da Dan Nwachiku na jamâiyyar Zenith Labour Party (ZLP) ya samu kuriâu 2,257.
Jamiâin tattara sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Adamawa ya sanar da cewa mutane 761,621 ne suka kada kuriâa a zaben kuma sun samu kuriâu 731,140.