fidelitybank

Atiku ya nemi goyon bayan wakilan PDP a zaben fidda gwani

Date:

Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, domin neman goyon bayan wakilan jam’iyyar gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a ranar 28 ga watan Mayu.

Atiku Abubakar ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP da suka hada da ‘yar takarar gwamna Ladi Adebutu, da shugaban jam’iyyar na jihar, Sikirullahi Ogundele, a sakatariyar jam’iyyar ta jihar.

Yayin da yake zayyana kuri’un wakilan, Atiku Abubakar ya ce, ya fi cancantar wakilci jam’iyyar da kuma mulkin kasa bisa kwarewa.

Ya bayyana cewa, idan aka zabe shi a kan karagar mulki, zai gudanar da mulkin Najeriya ne a kan wasu manifofi guda biyar, wato hadin kai, tsaro, tattalin arziki, ilimi da kuma ba da karin albarkatu da madafun iko ga sassan tarayya.

“Na yi alkawarin baiwa kowane bangare na kasar nan fahimtar zama kamar yadda muka yi a baya.

“Lokacin da muka hau mulki a 1999, mun fuskanci rashin hadin kai, kuma abu na farko da muka yi shi ne kafa gwamnatin hadin kan kasa wanda ya samar da zaman lafiya da muke bukata domin samun nasarar gudanar da mulki,” in ji shi.

Dan takarar ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro a fadin Najeriya, inda ya bayyana cewa hakan ne tushen ci gaban tattalin arzikin kasar.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp