Gabanin fara yakin neman zaben 2023 a ranar Laraba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nada tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Abubakar Bukola Saraki a matsayin masu taimaka masa na musamman a harkokin waje da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, a matsayin mai ba shi shawara na musamman.
Atiku a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa muhimman nade-naden masu ba shi shawara na musamman da nufin karfafa kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa.
Sanarwar ta kara da cewa a wani bangare na “wanda kuma aka nada a matsayin mashawarta na musamman ga dan takarar akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da kuma Sanata Ehigie Uzamere.
“An kuma nada tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus a matsayin mai baiwa dan takarar shugaban kasa shawara a fannin fasaha.
“Nade-naden za su fara aiki nan take.
Atiku Abubakar ya bukaci wadanda aka nada su yi amfani da kwarewarsu ta siyasa wajen tabbatar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.