Kungiyar mambobin Jam’iyyar PDP daga yankin Kudu maso Kudu da aka yiwa lakabi da kungiyar yakin neman zabe ta KARADE-MAZABU karkashin jagorancin Ada Fredrick Okwori, sun ziyarci Atiku Abubakar a gidan sa dake Abuja.
Da yake magana a yayin ganawar, daya Daga cikin ayarin Honorable Omoge Tamuno, ya ce, kungiyar tasu tana da yakinin cewar tsohon mataimakin shugaban kasar nada kwarewar da ake Bukata wajen tafiyar da mulkin kasar nan, kuma zai iya kubatar da ita daga halin da ta ke ciki sannan ya sake dora ta kan tafarkin zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewar Atiku yana cikin mutanen da suka farfado da tattalin arzikin kasar nan a baya.
Haka kuma, wani mamban ayarin ya bayyana Wazirin Adamawa a matsayin mutum wanda ya bada muhimmiyar gudummawa wajen bunkasar dimukuradiyya a Najeriya.
Mambobin ayarin sun kada kuri’ar goyon baya ga dan takarar shugaban kasar na PDP a zaben na 2023, inda ya ce sun yi kyakkyawan shiri domin samarwa Atiku Abubakar cikakken goyan baya Daga tushe.
Sanarwar da hadimin Atiku a kafafen yaɗa labarai, Abdulrasheed Shehu ya aikewa manema labarai ya ce, a nasa bangaren, dan takarar shugabancin na Najeriya ya yi marhabin da bakin, kuma ya gode musu bisa ziyarar, inda ya bukace su da jajircewa Wajen aiki domin nasarar Jam’iyyar PDP a zaben badi don kyakkyawar makoma ga Najeriya.
Mataimaki na Musamman ga Mai girma Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai.
10 ga watan Agusta 2022.


