Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga wadanda ‘yan fashin daji suka shafa a jihar Katsina.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Talata a lokacin da ya kai gaisuwar ban girma ga mai martaba Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumini Kabir Usman a fadarsa da ke Katsina, babban birnin jihar.
Atiku wanda ke Katsina a ci gaba da yakin neman zabensa na 2023, ya samu rakiyar abokin takararsa kuma gwamnan jihar Delta, Dokta Ifeanyi Okowa; shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu; Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal; Tsohon Gwamnonin Neja, Kano, Jigawa da Kaduna, Aliyu Babangida, Ibrahim Shekarau, Sule Lamido, Ahmed Maikarfi, da sauransu zuwa fadar sarki.
Ya jajanta wa al’ummar Katsina da sauran jihohin Arewa kan matsalar rashin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar yankin.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sha alwashin kawar da matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke addabar yankin idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar a babban zabe mai zuwa na 2023.
Ya ce: “Ina jajanta wa al’ummar Katsina da sauran jihohin Arewa da ke fuskantar kalubalen tsaro da tattalin arziki. Ina so in tabbatar muku da cewa idan aka zabe ni a matsayin shugaban Najeriya, zan kawo karshen wadannan kalubale.
“A madadina, ina bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga wadanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a jihar da suka koma wasu wurare a sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a cikin al’ummarsu.”