Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi kira ga dukkanin kungiyoyin da ke goyon bayan sa da su tashi tsaye domin samun nasarar jam’iyyar a zaben gwamna a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsayar da ranar 11 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar goyon bayan Atiku Abubakar, Oladimeji Fabiyi ya fitar a ranar Litinin, Atiku ya jaddada matukar bukatar lashe jihohin kasar nan zuwa PDP.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mai Girma Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) GCON ya umurci dukkanin kungiyoyin goyon bayan Atiku da ke da manyan tsare-tsare a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo da su tashi tsaye wajen zaburar da mambobinsu domin marawa jam’iyyar PDP a wadannan jihohin.
“Mambobi su tabbatar da cewa sun jajirce wajen zaben ‘yan takarar jam’iyyar, Mai Girma, Sanata Duoye Diri na Jihar Bayelsa, Sanata Sam Anyanwu (Sam Daddy) na Jihar Imo da Sanata Dino Daniel Melaye na Jihar Kogi.
“Mai girma Atiku Abubakar ya kuma jaddada matukar bukatar lashe wadannan jahohin ga jam’iyyar PDP. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa dukkan masu rike da tuta na PDP guda uku suna da hangen nesa, gogewar da ake bukata, da damar jagorantar PDP a zabe mai zuwa.”
Fabiyi ya bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ko shakka babu jam’iyyar PDP ta gabatar da jiga-jigan ‘yan takara masu karfin hali, gogewa da kuma iya shugabancin jihar.