Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da takarar neman shugaban ƙasa a babban zaɓe na 2023 mai zuwa a jam’iyyar adawa ta PDP.
Atiku, wanda ya shafe shekara fiye da 15 da suka wuce ya na neman shugabancin Najeriya, ya ce, zai mayar da hankali kan ɓangare uku idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
“A ƙarƙashin mulkina, zan mayar da hankali kan ɓangare biyar masu muhimmanci; haɗin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da ɓangarorin gwamnatin tarayya gaba da ƙara musu iko,” a cewarsa.
An gudanar da bikin a International Conference Centre da ke Abuja.