fidelitybank

Atiku ya janye ya bar wa Kwankwaso – NNPP

Date:

Peter Olagookun, shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar Ondo, ya jaddada cewa nasarar da jam’iyyar adawa ta shirya ta yi ya ta’allaka ne kan hadin kan manyan ‘yan jam’iyyar.
Ya yi imanin cewa ta hanyar hadin kai ne kawai za a iya kalubalantar jam’iyya mai mulki a zaben 2027.

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a birnin Akure, Olagookun ya bayyana cewa ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi tunanin komawa gefe don bai wa Rabiu Kwankwaso damar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa a 2027.

Kwankwaso, Abubakar, da Peter Obi sun kasance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun NNPP, PDP, da Labour Party (LP) a zaben 2023, bi da bi.

Duk ‘yan takarar uku Bola Tinubu na jam’iyyar APC ne ya kayar da su.

Tun bayan zaben dai ake ta rade-radin cewa akwai yuwuwar kawance tsakanin jiga-jigan ‘yan adawa uku na kalubalantar Tinubu a 2027, duk da cewa Kwankwaso ya musanta wadannan ikirari.

A ranar 20 ga watan Maris, Atiku ya tabbatar da cewa shi da sauran ’yan adawa za su kafa kawance don karbe mulki daga hannun jam’iyya mai mulki a shekarar 2027.

Olagookun ya bukaci shugabannin ‘yan adawa da su yi watsi da burin kashin kansu su marawa Kwankwaso baya a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.

“Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Alhaji Atiku Abubakar, Mista Peter Obi, Malam Nasir El-Rufai, da sauran masu fafutukar kafa kawancen ‘yan adawa su sa Atiku ya fice daga takarar shugaban kasa a 2027,” in ji Olagookun.

“Ya kamata ya marawa abokin aikinsa Kwankwaso baya, sannan kuma su zabi dan takara mai karfi daga Kudu a matsayin abokin takararsa, na yi imanin cewa da wannan tsari jam’iyya mai mulki za ta yi gwagwarmayar tinkarar ‘yan adawa”.

Sai dai Olagookun ya yi gargadin cewa idan ba tare da wannan matakin hadin kai ba, kungiyar za ta yi kasa a gwiwa kuma za ta wargaje kafin zaben 2027.

Ya kara da cewa “Idan Atiku ya koma gefe, tarihi zai gane rashin son kai da kishin kasa.” “Kwankwaso sahihin dan takara ne wanda zai iya jagorantar ‘yan adawa ga nasara a 2027.”

Olagookun ya kuma yabawa Atiku bisa kokarinsa na hada kan shugabannin adawa da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasa.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp