fidelitybank

Atiku ya janye daga duba kayan zaben INEC

Date:

Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar, PDP, Atiku Abubakar, shi da jam’iyyarsa sun janye sabuwar ƙarar da suka shigar ta neman tilasta wa hukumar zaɓe ba su damar duba kayan da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.

Atikun da jam’iyyarsa da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyya mai mulki APC a matsayin wanda ya ci zaɓen, sun shaida wa kotun musamman da ke sauraren ƙararraki kan zaɓen shugaban ƙasar a Abuja cewa ba su da buƙatar ci gaba da ƙarar.

Jagoran ayarin lauyoyin da ke wakiltar Atikun da PDP Mista Joe-Kyari Gadzama (SAN) shi ne ya shaida wa kotun haka lokacin da aka zauna fara sauraren ƙarar a yau Laraba.

Karanta Wannan: Wike ya caccaki Amaechi akan zabar Atiku maimakon Obi

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wani daga cikin lauyoyin na Atiku da PDP, wanda bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce tun da farko sun shigar da ƙarar ne saboda matsaloli da ƙalubalen da suka gamu da su lokacin da wakilan jam’iyyar da Atiku suka je hukumar zaɓen domin a ba su kayan su duba, kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

Ya ce, to kasancewar kafin a zo sauraren wannan ƙara da suka shigar ta tilasta wa INEC barin wakilan su duba kayan zaɓen, INEC da kanta ta fito ta yi alƙawarin ba su damar su je su duba wasu daga cikin kayan musamman ma takardar da aka yi zaɓe, ya ce saboda haka ne suka janye wannan sabuwar ƙara.

Atiku da jam’iyyar tasa da kuma ɗan takarar Labour shi ma da jam’iyyar tasa dukkaninsu suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na Najeriya, inda kowanne daga cikin ɓangaororin biyu ke iƙirarin shi ne ya yi nasara aka yi masa fashi, tare da lasar takobin ƙwato nasarar tasu a kotu.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp