Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da “zamewar” da Tinubu ya yi yayin a yake hawa bayan mota.
“Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyarsa lau.”
A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.
Yadda Tinubu ya fadi a bayan mota.
Is this real??? I hope he’s okay 😳😳😳
— Akpraise (@AkpraiseMedia) June 12, 2024