fidelitybank

Atiku ya gaza cika sharuɗan cin zaɓe – INEC

Date:

Hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta INEC, ta ce, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gaza cika sharuɗɗan da tsarin mulkin ƙasa ya gindaya kafin a ayyana shi matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

INEC ta bayyana haka ne a matsayin martani kan ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar ya shigar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Ta dai buƙaci kotun ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar ya shigar gabanta yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.

Karanta Wannan: Majalisa ta gayyaci Ministan kuɗi a kan ɓatan kuɗaɗen man fetur

Hukumar ta ce Atiku ya gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a aƙalla kashi biyu cikin uku na jihohin ƙasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja, wanda hakan na cikin sharuɗɗan cin zaɓe a ƙasar.

Game da ƙorafin saɓa dokar zaɓe, INEC ta ce an gudanar da zaɓen ne bisa dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ba tare da almundahana ba, kamar yadda masu ƙorafin suke zargi.

Hukumar zaɓen ta sake jaddada cewa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC shi ne halastaccen zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

Game da ƙorafin rashin samun rinjayen ƙuri’u a Abuja da ake yi wa Tinubu, INEC ta ce kundin mulkin Najeriya bai fitar da wani matsayi na musamman a kan ƙuri’un babban birnin ƙasar ba.

Domin haka, a cewarta ƙuri’un Abuja daidai suke da ƙuri’un kowacce jiha ta fuskar matsayi.

Atiku Abubakar tare da jam’iyyarsa ta PDP sun garzaya kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne domin ƙalubalantar sakamakon da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp