Dan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa Alhaji Atiku Abubakar (GCON), ya yi wata ganawa yau a Abuja da wani ayarin hadin gwiwa daga cibiyayar kasa da kasa ta republican da cibiyayar harkokin demukuradiyya ta kasa NDI karkashin jagorancin Mr. Frank LaRose sakataren jihar Ohio ta Amurka.
A taron, Wazirin Adamawa ya ce, ya yi ganawa mai muhimmancin gaske da ayarin, dangane da muhimmancin alfanun bunkasa dimukuradiyyar gaskiya a tsarin gudanar da zabe Musamman kare tsarin doka da oda da sauran batutuwa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ta Najeriya yace a yayin tattaunawar tasu, ya bada shawarar Samar da takardun zabe na Musamman domin kawar da matsalar sayen kuri’u Wanda ke Neman zama ruwan dare a tsarin zabukan mu.
A karshe taron, dan takarar ta PDP Atiku, ya godewa bakin nasa, bisa damuwar su da abinda ya shafi Najeriya. In ji mai taimaka masa a harkokin yada labarai, Abdulrasheed Shehu Uba Sharada.