fidelitybank

Atiku ya caccaki Tinubu a kan shekara guda kan karagar mulki

Date:

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran adawa, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ta ɗauka ba su sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa wahalhalu ba cikin shekara ɗaya.

Jim kaɗan bayan rantsar da shi a kan mulki, Tinubu ya ƙaddamar da wasu jerin sauye-sauye da zimmar farfaɗo da tattalin arziki, waɗanda daga baya suka haddasa hauhawar farashi da kuma ƙunci a ƙasar baki ɗaya.

Atiku ya ce tattalin arzikin ma baya ya koma a cikin shekara ɗaya ta mulkin Tinubu.

“Kamar yadda muka yi tsammani, cikin wata 12, Tinubu bai cka alƙawarin farfaɗo da tattalin arziki da kawo ƙarshen wahalhalu ba,” in ji shi cikin wata sanarwa da ya wallafa.

“Matakan da ya ɗauka da waɗanda bai ɗauka ba sun ƙara ta’azzara tattalin arzikin Najeriya. Har yanzu ƙasar na fama kuma ta ma fi tangal-tangal a yanzu sama da shekara ɗaya da ta wuce.

“Tabbas duka matsalolin – rashin aikin yi, da talauci, da wahalhalu – da suka mamaye gwamnatin Buhari sun ƙara ta’azzara.”

Idan ba a manta ba, daga cikin manyan matakan da Tinubu ya ɗauka har da sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, kodayake rahotonni na cewa har yanzu gwamnati na biyan tallafin.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp