Wata kungiya matsa a cikin jam’iyyar PDP, wato Concerned PDP League, CPDPL, ta yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023, da kada ya sake tsayawa takara a 2027.
Shawarar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu a ranar Lahadi kuma aka fitar a Abuja ta hannun sakatarenta na kasa, Alhaji Tasiu Muhammed da kuma mukaddashin daraktan yada labarai da sadarwa na kasa, Gbenga Adedamola.
CPDPL ta kuma bukaci shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, da kada ya sanya wani buri na neman kujerar shugaban kasa har sai 2031, don kaucewa sake afkuwar abin da ya faru da jam’iyyar a 2015 da 2023.
A cewar kungiyar, shawarar da ta bayar ya kasance masu sha’awar tsayawa takara daga Arewa su fahimci cewa Kudu tana da sauran shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewa a 2031.
“Shawarar mu kuma ita ce tabbatar da kwanciyar hankali a tsarin siyasar kasar,” in ji kungiyar.
Ta kuma shawarci jam’iyyar da ta yi taka-tsan-tsan da abubuwan da suka haddasa faduwarta a babban zaben 2023, tare da kauce musu yayin da take shirin tunkarar zaben 2027.
“Kamar yadda muka sani, shekarar 2023 shekara ce mai matukar kalubale ga babbar jam’iyyarmu, inda muka fadi zaben shugaban kasa saboda rashin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu na 2017, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, da gazawar shugabanci,” in ji CPDPL.