fidelitybank

Atiku hassada da baƙin ciki ya ke wa Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa

Date:

Fadar shugaban ƙasa ta ce, tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa, muƙamin da ɗantakarar jam’iyyar PDP na muƙamin a 2023, ta ce, yake ta faman nema har sau shida amma bai yi nasara ba.

Fadar shugaban ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙon Tweeter da ya sanya kwanan nan.

Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam’iyyarsa.

Sanarwar ta ƙara da cewa maganganu da shawarwarin da Atiku yake bayarwa a kan tattalin arziƙi sun nuna tsananin rashin fahimtarsa da ainahin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki, abin da sanarwar ta ce shi ne jagorancin Shugaba Tinubu ke magancewa.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...

Ni da Wike tif da taya ne – Fubara

Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce, babu...

Za a yi jana’izar Dantata a ranar Litinin

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid,...

Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 – Rahoto

Ƙungiyar fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam da tabbatar da dimokuraɗiyya...

Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan Dantata

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyarsa...

Dangantaka tsakanin Amurka da Canada ta yi tsami

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yanke dukkan...

An yi jana’izar Kwamandojin sojinta da masana nukiliyar Iran da Isra’ila ta kashe

Iran ta gudanar da jana'izar mutum 60, ciki har...

Za a binne Attaijirin dan kasuwar nan na Kano Dantata a Dubai

Allah ya yi wa attajirin ɗan kasuwar nan na...

Dalori ne ya maye gurbin Gnaduje a shugabancin APC

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa, Ali Bukar...
X whatsapp