fidelitybank

Atiku da Wike za su gwabza a gaban kotu

Date:

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da sansanin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike a yau a babbar kotun tarayya dake Abuja za su fara fafatawa a shari’a kan halalci ko akasin haka na zaben fidda gwani da ya haifar da Atiku.

Wani jigo a jam’iyyar Cif Michael Newgent Ekamon ne ya shigar da karar, inda ya bukaci kotun da ta kwace nasarar Atiku tare da bayyana Wike a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

Wata sanarwar sauraron karar da DAILY POST ta gani, ta nuna cewa mai shari’a Ahmed Ramat Mohammed ne ya sanya ranar sauraron karar.

Majiyoyi sun ce wasu manyan Lauyoyin Najeriya da har yanzu ba a san sunayensu ba Wike ya hada su, yayin da Ayo Kamaldeen Ajibade, Babban Lauyan Najeriya, SAN, zai jagoranci tawagar lauyoyin Atiku.

Takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022 tana kuma da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, jam’iyyar PDP da kuma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a matsayin wadanda suka amsa.

legit breaking news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp