Cif Stanley Osifo, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, a ranar Juma’a ya roki Alhaji Atiku Abubakar da Mista Peter Obi da su marawa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu goyon baya, domin ciyar da Nijeriya gaba.
Abubakar da Obi, ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party da Labour Party, sun sha alwashin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a gaban kotu.
A ranar Laraba ne dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.
Osifo, a wata sanarwa da ya fitar a Legas, ya ce Tinubu ne ya lashe zaben kamar yadda INEC ta bayyana.
Ya ce: “Tinubu a shirye yake ya karbi duk wanda ke da sha’awar aiwatar da kyakkyawan tsarin aikin Najeriya.
“Peter Obi da Atiku Abubakar gami da sauran ‘yan takarar da suka sha kaye a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, su hada kai da Bola Tinubu wajen ciyar da Najeriya gaba. ”