Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Yekeni Nabena, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ba zai iya mayar da al’ummar kasar cikin sahara ba.
Atiku ya zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da yin jabu a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.
Amma, Nabena, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce duk hayaniyar da ake yi game da takardar shedar jami’ar Jihar Chicago lamari ne da aka manta da shi kafin zaben.
Ya jaddada cewa ya kamata Atiku ya fara shirye-shiryen sake tsayawa takara a 2027 kamar yadda ya saba maimakon jawowa al’umma koma baya.
Nabena ya ce sabanin farfagandar da Atiku da jam’iyyun adawa ke yadawa a kafafen yada labarai, “Mai rejista na Jami’ar Jihar Chicago (CSU) Caleb Westberb bai taba cewa Shugaba Tinubu ya karya takardar shaidar da ya mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Najeriya ba.
Ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan da rahotannin zagon kasa da jam’iyyun adawa ke fitar da su domin kawo rudani da kuma neman a tausaya wa jama’a.
Jigon jam’iyyar ya ci gaba da cewa Nijeriya kasa ce mai ‘yancin kai, kuma har kotun koli ta kasa ta ce akasin haka, har yanzu shugaba Bola Tinubu shi ne wanda aka zaba bisa gaskiya kuma zai ci gaba da gudanar da harkokin kasar.
Nabena ya kuma ja kunnen alkalan Najeriya da kotun koli kan raina kotu da Atiku ya yi a kan lamarin da tuni ya shiga kotun.
Ya ce: “Bari in yi amfani da wannan kafar in gaya wa tsohon mataimakin shugaban kasa ya fara shirin wani zabe a 2027 kamar yadda ya saba. Zafafan siyasa kan al’amuran da suka shafi tunkarar zabe ba zai sa ya zama shugaban Najeriya ba.
“Ya kamata Atiku Abubakar ya sani yanzu ‘yan Najeriya sun ci gaba. A yanzu dai kasar na samun kyakkyawan shugabanci domin wannan gwamnati tana da riko da rikon amana.”