Ga dukkan alamu kungiyar malaman jami’o’in ASUU, za su fara taro, domin daukar kwararan matakai kan yajin aikin da ya kwashe sama da watanni shida ana yi.
A safiyar yau litinin cewa taron mai muhimmanci yana gudana ne a harabar jami’ar Abuja, inda shelkwatar ASUU take.
Duk da cewa wasu jami’o’in Jihohi sun riga sun janye yajin aikin, taron na yau na iya kawo karshen yajin aikin ko kuma ya tsawaita yajin aikin.
Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta dage kan shirin babu wani aiki ba albashi ga malaman jami’o’in da ke yajin aikin, lamarin da ya harzuka shugabannin kungiyar da ke karkashin Farfesa Emmanuel Osokode.


