fidelitybank

ASUU za ta gana da gwamnati kan shiga sabon yajin aiki

Date:

Shugabannin kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, da gwamnatin tarayya za su yi taron ganawa a ranar Litinin, domin shawo kan bukatun malaman jami’o’in tare da dakile yajin aikin da ke tafe.

A ranar Larabar da ta gabata ne kungiyar kwadagon ta fitar da sanarwar yajin aikin kwanaki 21 ga gwamnati inda ta bukaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta magance duk wasu matsalolin da ba a warware ba da ke kawo cikas ga ci gaban jami’o’in Najeriya.

Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar ASUU na kasa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a jami’ar aikin gona ta Michael Okpara da ke Umudike a jihar Abia.

A wani yunkuri na dakatar da yajin aikin da ya kunno kai, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya ce jami’an gwamnati za su gana da shugabannin kungiyar ASUU ranar Litinin.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da ya bayyana a shirin bayan kwana 100 da aka watsa a TVC ranar Alhamis.

“Mun riga mun aika sanarwa ga shugabannin ASUU domin mu hadu a ranar Litinin.

“A ranar Laraba, mu (bangaren gwamnati) mun duba wasikar da ASUU ta mika da kuma dukkan batutuwan da ke cikin wasikar. Fatanmu shine zuwa ranar litinin mu hadu a tattauna dasu.

“Wasu daga cikin batutuwan na tarihi ne; lokacin da kake magana game da yarjejeniyar 2009. Wannan wani abu ne wanda ya samo asali tun kusan 1981 lokacin da suka fara.

“Mun jima muna tattaunawa da shugabannin kungiyar ASUU kan al’amuran da suka shafi tsarin jami’o’in domin mu, tare, mu magance dukkan matsalolinsu,” inji shi.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp