Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu.
Ya ce, kungiyar ta lura da takaicin yadda kungiyar ta fuskanci yaudara mai yawa a mataki mafi girma a cikin shekaru biyar da rabi da suka gabata, inda ya ce gwamnatin tarayya ta tsunduma ASUU a tattaunawar da ba ta da tushe ba tare da nuna rikon amana ba.
“Saboda abubuwan da aka yi a baya, da kuma bayan tattaunawa mai zurfi kan martanin da gwamnati ta mayar kan kudurin ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, ya zuwa yanzu, NEC ta kammala da cewa ba a yi nasarar magance bukatun kungiyar ba.
“Saboda haka, NEC ta yanke shawarar sauya yajin aikin zuwa cikakken yajin aikin da zai fara daga karfe 12.01 na safe Litinin 29 ga Agusta, 2022,” sanarwar ta kara da wani bangare.
Ya kara da cewa: “NEC ta amince da kokarin da fitattun ‘yan Najeriya da kungiyoyi ke yi a baya da kuma na yanzu don shiga tsakani a rikicin da ya kunno kai. Ƙungiyarmu ta kasance a buɗe don yin aiki mai ma’ana kamar yadda muka saba yi.”
ASUU ta fara yajin aikin ne a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, bayan da gwamnatin tarayya ta ki biyan wasu bukatun ta.


