Bayan dogon zama da kungiyar malaman jami’o’in ta kasa ASUU ta yi cikin daren Lahadi, majalisar zartaswar kungiyar ta amince da tafiYA yajin aikin gargadi na wata guda, domin jan kunnen gwamnatin tarayya a amsa bukacinsu.
Vanguard ta rawaito cewa, wata majiya daga cikin ganawar ta ASUU ta ce, ta yanke wannan shawara ne, domin baiwa gwamnatin tarayya damar yin abinda ya kamata ko kuma su tafi yajin aikin din-din-din.
A cewar ta, “Kawai muna son baiwa gwamnati dama ne domin ta yi abinda ya dace, domin hana yajin aikin din-din-din. Mu ma fa iyaye ne, kuma ‘yayanmu na karatu a jami’o’in, amma ba zamu zuba ido harkar ilimi ta lalace a kasar nan ba.” .