Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU za ta kai karar gwamnatin kasar kan rijistar da ta yi wa sabbin kungiyoyi na malaman wato CONUA da NAMDA ( Congress of Nigerian Universities Academics, da National Association of Medical and Dental Academics).
Lauyan kungiyar ta ASUU, Femi Falana, shi ne ya bayyana haka a wata hira ta tashar talabijin na Channels, a yau Alhamis, inda ya ce za su kalubalanci yi wa kungiyoyin biyu rijistar.
A ranar Talata ne ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayar da takardar shedar rijista ga sabbin kungiyoyin biyu da ke zaman kamar kishiyoyi ga ASUU.
A lokacin da yake ba su takardar Ngige, ya ce kungiyoyin biyu za su wanzu kafada da kafada da ASUU.
Ita dai ASUU tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, inda mambobinta wato malaman jami’o’in gwamnati suka dakatar da aiki a kan kin biyansu kudaden alawus-alawus tare da neman kyautata jin dadinsu da sauran bukatu daga gwamnatin tarayya.