Biyo bayan umarnin da mahukuntan Jami’ar Jihar Benue (BSU) suka bayar a ranar Talata, inda suka umurci dukkan ma’aikatan da su koma aiki, nan take.
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU reshen Jihar Binuwai, ta yi kira ga mambobinta da su kwantar da hankalinsu tare da jiran umarnin shugabannin kungiyar.
Hukumar gudanarwa ta BSU a cikin wata sanarwa da magatakardar, Misis Mfaga Modom, ta fitar ta umurci dukkan ma’aikatan makarantar da su koma aiki nan take.
Amma da yake mayar da martani ga umarnin a wata sanarwa a ranar Laraba, ta hannun Terrumun H. Gajir, sakataren ASUU-BSU, ya shawarci mambobin kungiyar da su kwantar da hankula tare da jiran karin umarni.
Kungiyar ta yi gargadin cewa duk wani memba da aka samu ya sabawa yajin aikin zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.
A cewarsa, “ASUU-BSU na ci gaba da yajin aiki kamar yadda kungiyar ta kasa ta bayyana”, inda ya kara da cewa takardar ba ta shafi mambobinta ba.
Ya yi kira da a yi taron gaggawa a ranar Alhamis, 29 ga Satumba, 2022, domin tattauna hanyoyin da mambobin kungiyar za su bi.