Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin aikin da ta ƙudiri aniyar farawa a yau saboda rashin biyan mambobinta albashin watan Yuni.
Tun da farko ƙungiyar ta yi barazanar daina shiga azuzuwan ɗalibai saboda rashin biyansu albashin watan Yunin da ya gabata.
Ƙungiyar ta bayar da wa’adin cewa idan har ba a biya albashin watan a jiya Litinin ba, to za ta dakatar da shiga azuzuwan ɗalibai.
Jaridar Leadership a ƙasar ta ambato, shugaban ƙungiyar reshen Abuja, Dakta Sylvanus Ugoh na cewa an janye matakin ne saboda tuni gwamnati ta fara biyansu albashi.
“Mambobinmu sun fara samun albashinsu na watan Yuni tun a jiya kafin 12:00 na dare, wanda kuma shi ne wa’adin da muka bayar”, in ji shi.