fidelitybank

ASUU na iya shelanta yajin aikin sai baba-ta-gani

Date:

Majalisar zartaswar kungiyar malaman jami’o’i ta kasa za ta yi taro a yau Lahadi, domin duba yajin aikin da ke ci gaba da yi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin mambobin kungiyar ya ce: “Eh, mun hadu a yau kan yajin aikin da ake yi da sauran su.

Majiyar ta kuma ce, ba zai yiwu a janye yajin aikin ba, inda ta kara da cewa “Babu wani ci gaba mai kyau da na sani.”

Sai dai kuma shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, shi ma ya tabbatar da taron amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Taron dai na zuwa ne kwana daya da kare yajin aikin gargadi na wata daya da kungiyar ASUU ta yi.

Wata majiya da ta zanta da PM News ta ce, kungiyar na iya shelanta yajin aikin sai baba-ta-gani saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza magance matsalolin da ASUU ta gabatar.

Kungiyar ASUU ta zargi gwamnatin kasar da gaza aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattabawa kungiyar a shekarar 2009.

Kungiyar ta ASUU ta kuma zargi gwamnatin tarayya da yunkurin kin tura UTAS, tsarin biyan kudi da ASUU ta tsara a madadin tsarin biyan kudin IPPIS.

nigerian 
newspapers today the sun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...
X whatsapp