Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su duba halin da daliban ke ciki, su janye yajin aikin da suke yi.
Ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a bikin ranar samar da albarkatu na kasa karo na 19 da kuma bayar da lambar yabo ta kasa ga fitattun ‘yan Najeriya 48 da kungiyoyi a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar mai take, ‘A bikin karramawar ranar samar da albarkatu ta kasa, shugaba Buhari ya roki ASUU da ta janye yajin aikin.