Kotun Daukaka kara ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU, da ta gaggauta komawa bakin aiki ba tare da bata wani lokaci ba.
Hukuncin ya biyo bayan daukaka karar da kungiyar ta yi ne a kan hukuncin da Kotun Kwadago ta kasar ta yi ne inda ta umarci kungiyar ta ASSU da ta kawo karshen yajin aikin da ta kwashe wata bakwai tana yi.
Yayin yanke hukuncin kotun daukaka karar ta ce janye yajin aikin shi ne sharadin kawai da zai sa ta samu damar daukaka kara da ta yi kan hukuncin kotun kwadagon.
A kan hakan ne kotun ta yarda ta saurari daukaka karar amma da sharadin kungiyar ta janye yajin aikin da take yi ba tare da bata wani lokaci ba, kafin a kai ga warware ainahin shari’ar da ake yi kan batun.
Ita dai ASUU tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, inda mambobinta wato malaman jami’o’in gwamnati suka dakatar da aiki a kan kin biyansu kudaden alawus-alawus tare da neman kyautata jin dadinsu da sauran bukatu daga gwamnatin tarayya.
Gwamatin tarayya ta yi wa wasu sabbin kungiyoyi biyu na malaman jami’a da suka bullo wadanda ke zaman tamkar kishiya ga ASUU.
Kungiyoyi su ne CONUA da NAMDA ( Congress of Nigerian Universities Academics) da (National Association of Medical and Dental Academics).
Kuma ASUU ta ce za ta kai gwamnati kara kan yi wa kungiyoyin biyu rijista.