Sabuwar kungiyar ma’aikatan koyarwa a jami’o’i ta kasa da gwamnati ta yi wa rijista, ta yi kira ga takwararta kungiyar ASUU ta cimma masalaha da gwamnati don dalibai su koma daukan darasi a azuzuwa.
Sabuwar kungiyar ta ce ita ba ta yajin aiki, duk da haka tana kira ga gwamnatin tarayya da takwararta kungiyar ASUU su sasanta tsakaninsu ta yadda za a bude jami’o’i, don harkokin koyo da koyarwa su ci gaba.
Babban jami’in kungiyar CONUA na kasa, Niyi Sunmonu ne ya yi wannan kira lokacin da yake zantawa a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talbijin din Channels a ranar Laraba.
Jami’in ya kuma yi kira da a rika tuntubar dukkan kungiyoyi masu rijista cikin harkokin da ake da wata matsala game da su. A ranar Talata ne, ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige ya bai wa kungiyar CONUA da ta NAMDA rijistar zama halattattun kunyoyin malaman jami’o’i a kasar.
Tashar Channels ta ambato ministan yana cewa kungiyoyin biyu za su rika gudanar da harkokinsu ne tare da ASUU, haka kuma sabbin kungiyoyin za su ci gajiyar duk wani hakki da alfarma kamar yadda ake bai wa duk wata kungiyar malaman manyan makarantu.
Tun a tsakiyar watan Fabrairun 2022 ne kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki don nuna bijirewa kan rashin biyan kudade alawus-alawus da rashin kyautata jin dadin malamai da sauransu.