fidelitybank

ASUU ba su da hujjar cigaba da yajin aiki – Badaru

Date:

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce, kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ba ta da wasu dalilai da za su iya ci gaba da yajin aikin.

Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manyan sakatarorin dindindin, daraktoci, mataimakan daraktoci, da shugabannin ma’aikatu da na kananan hukumomi a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake Dutse.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan yajin aikin da kungiyar ASUU Sule Lamido ke yi, reshen Kafin-Hausa a jihar Jigawa.

Ya bayyana cewa ASUU a jami’ar mallakar gwamnati ba ta da dalilin ci gaba da yajin aikin.

“Ban ga dalilin da zai sa jami’o’in jihar su ci gaba da yajin aikin saboda kamar yadda gwamnatin jihar ta riga ta biya musu bukatunsu kamar lokacin da ya kamata.

“Kusan kashi saba’in cikin dari na Malamai ‘yan asalin jihar ne da suke tunanin nuna kauna da damuwa ga ilimin shugabanni masu zuwa,” in ji shi.

Gwamna Badaru ya bukaci kungiyar da ta yaba da jajircewar gwamnati kada a yi amfani da su wajen yakin da bai shafe su ba.

Don haka ya bukaci dattawa da sauran masu ruwa da tsaki a jihar su sa baki a yajin aikin da ake yi.

ASUU ta shiga yajin aikin ne a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kan batun shigar ma’aikatan gwamnatin tarayya a IPPIS, sai dai jami’o’in gwamnatin jihar ba su da alaka da IPPIS tunda albashin su baya zuwa daga gwamnatin tarayya.

guardian newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp