A ranar Lahadi ne kungiyar Super Falcons ta Najeriya za ta fara shirye-shiryen tunkarar wasan karshe na neman gurbin shiga gasar Olympics ta 2024 da Afrika ta Kudu.
Tuni dai babban kociyan kungiyar Randy Waldrum ya gayyaci ‘yan wasa 22 domin fafatawar ta biyu.
Tawagar da ke da rinjayen ‘yan wasa daga kasashen waje za su hallara a Abuja ranar Lahadi don fara shirye-shiryen tunkarar wasan.
Taurari na yau da kullun, Asisat Oshoala, Chiamaka Nnadozie, Rasheedat Ajibade, Ashleigh Plumptre, Michelle Alozie da Toni Payne na daga cikin ‘yan wasan da Waldrum ya gayyata.
Super Falcons na neman komawa gasar Olympics bayan shafe shekaru 16 ba a buga gasar ba.
Za a yi wasan farko ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranar Juma’a 5 ga Afrilu.
Kungiyoyin biyu za su kara ne a fafatawar da za a yi a Pretoria a ranar Talata 9 ga Afrilu.