Aston Villa za ta dauki Mauricio Pochettino, domin ya maye gurbin Steven Gerrard in ji The Telegraph.
Shi dai Gerrard na fuskantar kalubale a kakar bana, bayan da Aston Villa ke kasa taka rawar gani a kakar nan.
Villa tana ta 16 a kasan teburi mai maki tara, bayan cin wasa biyu da canjaras uku da shan kashi a karawa biyar.
Kungiyar da Villa ta ci a bana a Premier sun hada da Evrton da Southampton, yayin da ta yi canjaras da Manchester City da Leeds United da kuma Nottingham Forest da kowa ke kwasar garabasa.
Kungiyoyin da suka doke Villa a wasa 10 da ta buga a Premier kakar nan, sun hada da Bournemouth da Crystal Palace da West Ham da Arsenal da kuma Chelsea.
Pochettino, wanda Paris St Germain ta kora kan kakar bana, ya koyar da Tottenham tsakanin 2014 zuwa 2019.
Kociyan ya fara horar da tamaula a Espanyol daga 2009 zuwa 2012 daga nan ya koma jan ragamar Southampton daga 2013 zuwa 2014.
Gerrard wanda ya koma Aston Villa ranar 11 ga watan Nuwambar 2021 ya ja ragamar wasa 39 da cin 13 da canjaras takwas aka doke shi karawa 18.