fidelitybank

Asibitin Aminu Kano ya yi tir da likitan da ya yi sakaci da lafiyar jariri

Date:

Hukumar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ta yi Allah wadai akan sakacin da wani likita ya yi lokacin da yake kula da lafiyar wani jariri.

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun, Hauwa Muhd Abdullahi, Shugabar Sashen Hurda da Jama’a na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ta ce, Jaririn wadanda aka haifa makon da ya gabata ya zo da wata matsala wadda ta bukaci yi masa gwaji ta hanyar daukar jininsa a inda likitan ya shiga dimuwa wanda ya haifar da abin da ya faru.

Hukumar Asibitin ta girgiza da Jin Wannan mugun labari Wanda a shekaru talatin da uku da kafuwar Asibitin Hakan bai tabar faruwa ba. Hukumar tana jajentawa iyayen wannan jariri bisa ga abin da ya faru.

A Kuma halin da ake ciki an mika wa kwamitin da yake bibiyar matsalolin badakala da sakacin aiki wato (Committee on Negligence of Duty)domin yin zurzurfan bincike tare da daukan mataki akan duk Wanda yake da hannu a cikin wannan sakaci da ya faru.

Shugaban Asibitin Koyarwan farfesa Abdurrahman Abba Sheshe, ya yi kira ga duk mara lafiya ko Yan Uwan marasa lafiyan da su ga ba su gamsu da yadda ake kula da lafiyar su ko ta Yan Uwansu ba, da su yi gaggawa wajen sanar da hukumar Asibitin ta Hanyar jami’anta wadanda ake kira da( Servicom Desk Officers).

Ya ce, Asibitin yan a da irin wadannan jami’i kimanin Arbanin, wadanda aka raba su a sassan gudanar da aiki daban daban a cikin Asibitin.Baya ga sashen hurda da Jama’a da wajen Matron-Matron na dakin kwanciya wadanda suke aiki tsawon awa ashirin da biyar.
Farfesa Abdurrahman,ya kara da cewa ta Hanyar mika korafi ne kawai hukumar Asibiti za ta iya kamowa tare da hukumta masu laifi.

Ya Kuma Yi kira ga Mahaifin wannan jariri da ya taimaka wajen isar da makamancin wannan korafi ga kwamitin binciken ko Kuma sashen hurda da Jama’a na Asibitin.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp