Likitoci a asibitin kashi na Dala a birnin Kano na gudanar da tiyata irinta ta farko ta sauya kashin kafada ga wata mata.
Hotuna daga asibitin dai sun nuna yadda tawagar likitocin suke gudanar da shirye-shiryen yin wannan aiki.
Kafin yau din dai ba a taba gudanar da irin wannan aiki ba a Najeriya, inda wasu ke kallon hakan ka iya rage yawan ficewa daga kasar zuwa kasashen waje domin neman lafiya.